Poems

Wasiyya Sipikiyya

Ta'ala ina rokonka ranar da zan cika

Kasa in cika Allah cikin daki na
 
Gaban duk iyali na da 'ya'ya da 'yan'uwa
Allah ina rokon ka sai a gidana
 
Idan na cika yan'uwa na gaya muku
Da kun ji cikawata ku taru gidana
 
Idan har da rana abin yazo ko cikin dare
Batun jinkiri kar dai ya faru wurina
 
Idan anyi sallah an gama kar a dakata
A dauka kawai hanyar zuwa kabarina
 
Idan anka je da zuwa a sani ciki kawai
Cikin hankali domin tuno lamarina
 
Kasar kabarin kuma kar a ware daban-daban
A turo gaba daya duk ta watsu a kaina
 
Idan aka kare gini da an tashi an gama
Ku koma wajen harkarku ya jama'ata
 
Batun sadakar Uku, ko Bakwai, ko ta Arba'in
Kaza shekara wallahi babu ruwana
 
Irin masu kukan nan da ihu da razana
Don Allah na roke ku kar kuyi kaina
 
Ina tausayin ku kwarai zuwa gun jana'iza
Kaza wahalar tafiya hakan kabarina
 
Kaza wahalar wanka da dauko ni don zuwa
Cikin makara tafiya zuwa karshe na
 
Hakika a rannan da da ikon da zan iya
Ya sa tausayin a wajen dukan jama'ana
 
Anan zan tsaya domin wasiyarmu ta tsaya
Mudi Spikin ne uba ga Amina